5 Agusta 2020 - 12:42
​Lebanon: Mutane 100 Ne Aka Tabbatar Da Mutuwarsu Sakamakon Fashewar Wasu Abubuwa A Beirut

<p "="">Akalla mutane 100 ne aka tabbatar da mutuwarsu yayin da wasu fiye da 4000 kuma suka jikkata, sakamakon tarwatsewar wasu sanadarai masu fashewa a birnin Beirut fadar mulkin kasar Lebanon a yammacin jiya.

ABNA24 : Ministan lafiya na kasar ta Lebanon ya fadi a daren jiya, adadin mutanen da aka tabbatar da mutuwarsu ya zuwa yanzu sun kai 78, yayin da fiye da 4000 kuma suka samu raunuka, amma sabbin rahotanni a yau na cewa adadin wadanda suka mutu ya kai 100.

A nasa bangaren shugaban hukumar tsaro ta cikin gida Abbas Ibrahim ya bayyana cewa, ga dukkanin alamu wasu sanadarai ne masu tarwatsewa da aka ajiye a gabar ruwan Beirut suka tarwatse, wanda hakan ya girgiza birnin na Beirut baki daya.

Yanzu haka dai asibitocin birnin Beirut sun cika da mutane da suka samu raunuka, inda ake jinyar wasu a cikin motocin daukar marassa lafiya.

Kasashen duniya da dama sun yi wa kasar Lebanon tayin bayar da taimakon gaggawa, daga cikin kasashen har da Qatar, Iran, Turkiya, Faransa , Burtaniya da sauransu.

Da jjifin safiyar yau Laraba bukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar Rasha ta aike da manyan jiragen sama guda 5 dauke da ma'aikata da kuma kayan aiki zuwa birnin Beirut, domin taimaka wa wajen gudanar da ayyukan agaji na musaman cikin gaggawa.

342/